Ɗan shekara 17 ya hallaka kansa a Benue

0
210
Yan sanda
Yan sanda

Rundunar ƴan sandan jihar Benue ta tabbatar da mutuwar wani yaro matashi ɗan shekara 17 wanda ya hallaka kansa kusa da Makurdi, babban birnin jihar.

Mai magana da yawun ƴan sandan jihar SP. Catherine Anene, ta tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin, inda ta ce matashin ɗan makarantar sakandari mai suna Terhemba Tyochivir, ya kashe kansa ne a ranar Alhamis bayan tashi daga makaranta.

Sai dai babu ƙarin bayani kan abin da ya janyo matashin ya kashe kansa ba.

Jaridar DailyTrust ta ruwaito shaidu na cewa bayan an ga gawar matashin ne, aka garzaya da shi wani asibiti da ke babban birnin jihar, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here