An kwashe sojojin Mali bayan wani hari da aka kai wa sansaninsu

0
144

An kwashe sojoji daga wani sansaninsu da ke arewacin Mali, bayan wani da ‘yan bindiga suka kai, a cewar rundunar sojin kasar.

Wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce dakarun na Mali sun wargaza shirin maharan a Acharane, wani yanki da ke birnin Timbuktu mai tsohon tarihi.

Babu bayani a fayyace a kan ko maharan, ‘yan ta-da-kayar-baya masu ikirarin jihadi ne ko kuma Azbinawa ‘yan tawaye.

Duka bangarorin biyu sun kara yawan hare-haren da suke kai wa a cikin ‘yan makonnin nan – a daidai lokacin da dakarun kwantar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya ke janyewa daga kasar bayan shugabannin mulkin sojin Mali sun nemi su fice.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here