Karen shugaban Amurka, Joe Biden, wanda ake yi wa laƙabi da ‘Kwamanda‘, ya sake cizon wani jami’in tsaro na sirri wanda ke cikin masu kare lafiyar shugaban ƙasar.
Lamarin ya faru ne a ranar Litinin da daddare, inda aka bai wa jami’in kulawa a wajen da lamarin ya faru, kamar yadda wata sanarwa ta ƙunsa.
Wannan ne karo na 11 da karen ke cizon jami’an tsaro a fadar ta White House.
A baya, sakataren yaɗa labarun fadar White House ya ɗora alhalkin faruwar lamarin kan gajiya sanadiyyar ayyukan da ke gudana a fadar.
Karen shi ne ƙarami a cikin jerin karnukan iyalin shugaban ƙasar.
Wasu lokutan da aka samu rahoton cizon karen sun faru ne a gidan shugaban ƙasar da ke Delaware.
A watan Yulin da ya gabata, jamai’an fadar White House sun ce suna shirin bai wa karen horo bayan yunƙurin da ya yi na cizon ma’aikata.
