An lakadawa jarumar TikTok Murja Kunya duka a Kano

1
272

Wasu da ba a san ko suwaye ba sun yi wa fitacciyar matashiya ‘yar Tiktok din nan Murja Ibrahim Kunya dukan tsiya a yammacin yau a Kano.

A hotunan matashiyar da suka bayyana a shafukan sada zumunta da har Hausa24 ta samu gani bata-garin sun canza mata kama da raunuka a fuskarta.

Tuni dai aka fara yin kira ga jami’an tsaro da su bi mata hakkinta ta hanyar zakulo wadanda suka yi mata wannan aika-aika.

Murja Ibrahim Kunya dai tayi kaurin suna a shafin TikTok inda take da mabiya masu dimbin yawa,dake bibiyar shafin nata.

1 COMMENT

  1. Baki shi yake yanka wuya, Murja Bata da Tarbiyyar Magana… Ko Masoyan wadanda take Cin mutuncin zasu iya Yi mata dukan Jan kunne.

    SHAWARA:
    Ta dinga Tauna Magana kafin ta fitar, Haramun ne Cin mutuncin mutum a Bainar Jama’a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here