Ana tuhumar Sylvia Bongo Ondimba Valentin, ‘uwar gidan hambararren shugaban kasar Gabon, Ali Bongo Ondimba da laifukan wawaso ga dukiyar kasar, kamar yadda mai gabatar da kara ya bayyana, wata guda kenan bayan juyin mulkin da sojoji suka yi.
Lauyan masu shigar da kara, Andre Patrick Roponat, na tuhumar ta da halasta wa kanta kudin haramun.
“An kama wasu ‘yan kasar guda goma sha biyu da ake tuhuma da aikata laifuka, inda wasu daga cikin su ke tsare a gidan yari. A cikin wannan yanayi ne Madame Sylvia Bongo Ondimba Valentin ta bayyana a gaban majistare a ranar 28 ga watan Satumba 2023. Ana tuhumar ta da laifin karkatar da kudade, karbar kayan sata da kuma aikata zamba, kuma wadannan laifukan sun ci karo da sashe na 116, 117, 312 da 380 na kundin laifuffuka,” a cewar Andre Patrick.
Matar tsohon shugaban kasar dai an haramta fita daga Gabon, tun bayan da aka hambarar da mijinta a ranar 30 ga watan Agusta.
A lokacin da aka kifar da gwamnatin Bongo, fadar shugaban kasar ta ce Valentin tana tsare a gidanta da ke Libreville, amma lauyoyinta da ke Faransa sun ce an tsare ta ba bisa ka’ida ba.
Ali Bongo, wanda da farko aka tsare shi a Libreville bayan juyin mulkin, daga bisani gwamnatin mulkin sojin ta bashi ‘yancin tafiya kasashen waje domin neman lafiyarsa.
Tuni dai aka tuhumi danta Noureddin Bongo Valentin da laifin almundahana da dukiyar al’umma tare da wasu tsoffin ministoci biyu.