Wasanni: Labaran kwallon kafa a yau Juma’a

0
134
Ball

Kocin Liverpool Jurgen Klopp na son ɗan wasan Borussia Dortmund, Donyell Malen mai shekara 24, bayan taka rawar gani a farkon kaka, kuma ƙungiyar ta Bundesliga na neman fam miliyan 52 a cinikin.

Chelsea na sa ido domin ganin yadda za ta kaya tsakanin Victor Osimhen da Napoli, yayin da suke zawarcin ɗan wasan na Najeriya mai shekara 24.

Kungiyar Al Hilal ta Saudiyya na ci gaba da matsa kaimi kan Osimhen a wata yarjejeniyar ta ba shi fam miliyan 39 kowacce shekara tsawon shekaru biyar da kuma biyan Napoli kudaden da take nema na fam miliyan 173.

Juventus na son saye ɗan wasan Denmark Pierre-Emile Hojbjerg, mai shekara 28, daga Tottenham a watan Janairu.

Kocin Liverpool Jurgen Klopp na son ya tswaita kwantiragin ɗan wasan Sifaniyar nan da ke buga tsakiya Thiago Alcantara.

Akwai rashin tabbas kan makomar ɗan wasan Holland, Ian Maatsen da ke taka leda a Chelsea.

Manchester United da Chelsea na harin ɗan wasan Brazil da Flamengo, Lorran mai shekara 17.

Tsohon kocin Real Madrid Zinedine Zidane, mai shekara 51, ya amince da wata yarjejeniyar da ‘yan Saudiyya da ke kokarin ganin sun saye ƙungiyar Marseille.

Steve Bruce, mai shekara 62, na iya komawa aikin horarwa a Jamhuriyar Ireland, yayin da ake matsa kaimi kan kocinsu na yanzu Stephen Kenny.

Arsenal na fatan cimma yarjejeniya da ɗan wasan Ingila Ben White, mai shekara 25, a sabon kwantiragi.

‘Yar wasan Arsenal ta mata Katie McCabe na gab da cimma sabuwar yarjejeniya da ƙungiyar, yayin da Chelsea da Manchester City da Bayern Munich ke harin matashiyar ‘yar shekara 28.

Ana tattaunawa tsakanin Newcastle da ɗan wasan gaba na Brazil Joelinton, mai shekara 27, kan sabon kwantiragi.

Ɗan wasan Brentford Ivan Toney na son samun sabuwar dama a 2024, yayin da ake tunanin Arsenal da Chelsea za su neme shi a baɗi.

Patson Daka dan Zambia da ke taka leda a Leicester ya kasance wanda Brentford ke son maye gurbin Toney da shi.

Chelsea na shirin gabatar da tayi kan ɗan wasan Sifaniya, Marc Cucurella mai shekara 25 kan Janairu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here