Jerin ministoci: Tinubu ya maye sunan El-Rufa’i, ya mika wa majalisa sunayen mutum 3

0
201
Tinubu
Tinubu

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya mika sunayen wasu karin ministoci uku ga majalisar dattawa inda ya nemi a tantance su a matsayin ministoci.

Shugaban majalisar, Godswill Akpabio, ne ya bayyana hakan yayin da yake karanta wasikar shugaban kasa a zauren majalisar a ranar Talata.

Mutanen uku da aka zaba sun hada da Dokta Jamila Bio daga jihar Kwara da Olawale Olawande daga jihar Legas, wadanda aka zaba a matsayin ministocin ma’aikatar matasa.

Mutum na uku, Balarabe Abbas, shi ne zai maye gurbin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, wanda majalisar dattawa ta ki amincewa da tabbatar da shi a kan takardar shaidar tsaro.

Bayan majalisar dattawa ta tabbatar da shi, Abbas za a tura shi ma’aikatar muhalli, wacce aka kebe don jihar Kaduna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here