Kotun zaben Kano: DSS ta cafke matar da ta yi wa Shettima, Gawuna da alkalin kotun barazana

0
143

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kama wata mata bisa zargin yin barazanar kashe kanta da kuma wadanda ta ce, su ne suka shirya aka kwace nasarar Gwamna Abba Kabir aka baiwa dan takarar gwamna a jam’iyyar APC a jihar Kano, Nasiru Gawuna, a kotun sauraron kararrakin zabe.

A baya, Leadership ta rahoto cewa, kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kano ta bayar da umarnin janye takardar shaidar lashe zabe da aka baiwa gwamna Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP tare da bada umarnin mayar da nasarar ga dan takarar gwamnan APC a zaben ranar 18 ga watan Maris, Dakta Nasir Gawuna.

A cewar wani rahoto da wata jarida ta yanar gizo, Newspoint Nigeria ta wallafa a ranar Talata, matar mai suna Fiddausi Ahmadu, mai shekaru 23, ta yi ikirarin cewa, ita mai fafutukar kare hakkin jam’iyyar NNPP da Gwamna Yusuf ce a wani faifan bidiyo da aka watsa.

A cikin faifan bidiyon, an ji Fiddausi acikin Harshen Hausa tana barazana ga shugaban kotun, inda ta yi gargadin cewa duk inda ta ga Alkalin, ba za ta damu ba ta yi kunar bakin wake tare da shi ba.

Har ila yau, ta kuma sake yin irin wannan barazanar ga Dakta Nasiru Gawuna da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here