Girgizar kasa ya hallaka sama da mutum 1,500 a Afghanistan

0
210

Ma’aikata na ci gaba da ayyukan ceto mutanen da suka kubuta daga girgizar kasa mai karfin gaske da ta ritsa da kauyukan Afganistan, inda ta kashe mutane fiye da 1,000.

Girgizar kasar mai karfin awo 6.3 ta auku ne da safiyar Asabar a lardin Herat, wani wuri maras kyawu da ke cike da gidajen kasa.

Mazauna kauyuka a yankin, na ci gaba da amfani da shebura da hannaye wajen zakulo wadanda suka bace mutane sama da 500, in ji Majalisar Dinkin Duniya.

Taimako da kuma layukan sadarwa da suka fuskanci ƙalubale sun fara shiga a ranar Litinin.

Girgizar kasar ta faru ne a Zindajan, wani yanki na karkara mai tazarar kilomita 40 daga birnin Herat, inda aka kiyasta cewa “kashi 100 na gidaje sun lalace gaba daya,” a cewar ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya.

Hotunan kauyukan sun nuna daukacin gidajen da ba su da karfin jure irin wannan girgizar kasar, sun zama ɓaraguzai.

“Mun dawo gida sai muka ga babu abin da ya rage, komai ya zama laka,” wani mazaunin garin Nek, Mohammad ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

“Sai muka fara tona lakar da shebur, da kuma duk abin da za mu iya amfani da shi don ceto mata da yara daga baraguzan gine-gine.”

Tun farko dai gwamnatin Taliban da hukumomin agaji sun yi ta kokarin tantance adadin wadanda suka mutu, ko kuma nawa ne suka bata.

Da wuya jami’ai su samu bayanan yawan jama’ar irin waɗannan ƙauyuka masu nisa.

Har ila yau yankin na da al’ummomin da yaki da fari suka raba da muhallansu, lamarin da ya sa da wuya hukumomin yankin su iya sanin hakikanin adadin mutanen da ke zaune a wurin.

Asibitocin da ba su da kayan aiki, sun yi ta kokawa wajen daukar mutanen da suka jikkata, wadanda a yanzu sun haura sama da mutum 1,600.

An aika da yawa daga cikinsu zuwa Asibitin Lardin Herat, inda ƙungiyoyin agaji kamar Médecins Sans Frontières (MSF) suka kasance tun ranar Asabar.

Prue Coakley, mukaddashiyar wakiliyar kungiyar a Afganistan ta ce “An yi sa’a, yawancin majinyatan da ke zuwa, bukatunsu ba na gaggawa ba ne.” “Duk da haka, yawancinsu ba su da gidajen da za su koma, shi ya sa da yawa a cikinsu ke ci gaba da zama a asibiti.”

Ta kara da cewa an tura ayarin da ke mayar da hankali a kan yara majinyata da ke zuwa asibiti a Herat.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akasarin wadanda suka kubuta a girgizar kasar, kuma aka kwantar da su a asibitoci, mata ne da yara kanana, yayin da likitoci suka shaida wa BBC cewa mata da kananan yara su ma suna da yawa a cikin wadanda suka mutu.

Gwamnatin Taliban ta ce wadanda suka kubutan na bukatar abinci da ruwan sha da magunguna da tufafi da tantuna a cikin gaggawa.

Hukumomin agaji da suka hadar da kungiyar agaji ta Red Cross a Afghanistan, da Médecins Sans Frontières (MSF), da shirin samar da abinci na duniya da kuma Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Dinkin Duniya (Unicef) sun tura kayan agaji.

Sai dai hukumomin sun ce ƙasar da ke da karancin kuɗi na buƙatar karin taimako.

Afghanistan dai na fama da matsalar tattalin arziki tun bayan da kungiyar Taliban ta karbe iko a 2021, lokacin da aka dakatar da tallafin kai tsaye ga gwamnati.

Kasashe kadan ne suka yi alkawarin ba da tallafin kudi tun bayan aukuwar girgizar kasar a ranar Asabar. Kungiyar ba da agajin Red Cross ta China ta yi tayin bayar da dala 200,000, a matsayin taimakon kudi na gaggawa, in ji kafofin yada labarai.

Makwabciyarta Pakistan ta ce tana tuntubar jami’an Afghanistan, kuma za ta ba da dukkan goyon baya ga kokarin farfado da kasar.

Afganistan na yawan fuskantar girgizar kasa musamman a tsaunin Hindu Kush da ke kusa da mahadar farantin Yura-asiya da Indiya.

A cikin watan Yunin bara, lardin Paktika ya fuskanci girgizar kasa mai karfin awo 5.9 wadda ta yi sanadin mutuwar mutane sama da 1,000, tare da raba dubun dubatar wasu da matsugunansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here