Yadda Kwankwaso da Abba suka jagoranci auren gatan mutum 1,800 a Kano

0
150

Gwamnatin jihar Kano Karkashin jagorancin, Abba Kabir Yusif ta kaddamar da auren zawarawa 1,800 wanda aka gudanar a Babban Masallacin Juma’a na Gidan Sarkin Kano.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tare da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da Mataimakin sa Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ne, suka jagoranci daurin auren.

Haka zalika, an daura da auren sauran zawarawan a kananan hukumomin Jihar Kano 44, wanda aka gudanar a masallatan Juma’a na shelkwatar kananan hukumomin.

Da yake Karin haske jim kadan da daura auren zawarawan karamar hukumar Kunchi, babban limamin karamar hukumar Kunchi, Imam Gwani Nazifi Abubakar, ya taya angwaye da amaren murnar sannan ya bukace su da su zauna da juna cikin aminci da amana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here