Abubuwan da shugaban kasa ya wajabta min yinsu – Ministan yada labarai

0
145

Ministan yaɗa labarai da wayar da kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce, Shugaba Tinubu ya ɗora masa nauyin jaddada tasirin kishin ƙasa, aiki da gaskiya da kuma kawar da nuƙu-nuƙu, a matsayin kyawawan ɗabi’un da gwamnatinsa za ta ɗore kan turbar su.

Ministan ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), a Abuja.

Ya ce, ajandar Fata Nagari Lamiri da gwamnatin Shugaba Tinubu ta hau mulki da ita, wani kyakkyawan muradi ne na ɗaukaka Nijeriya zuwa ƙololuwar nasara da bunƙasa a cikin manyan ƙasashe na duniya, tare da shafe baƙin fentin da ake kallo a jikin wannan ƙasar.

Idris ya ce, Tinubu ya hore ni da kafuwa wurin ganin mun samu nasarar wayar da kan ‘yan Nijeriya cikin shekaru kaɗan masu zuwa, ta yadda aƙalla za mu iya sake kankaro ƙima da martabar ƙasar nan, tare da fara ɗorawa bisa kyakkyawar turbar da ta fi dacewa mu bi.

“Wannan kuwa babban kalubale ne. Saboda kun dai san ba a zukatan matasa kaɗai ɗa’a da kishi su ka yi ƙaranci ba, har ma a zukatan yara da manya.

“Ina ganin dalili kenan da ya sanya shugaba Tinubu  ya canja sunan Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Bunƙasa Al’adu, zuwa Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai.

“Hakan, ya na nufin shugaban ƙasa na so ɗora batun wayar da kai da cusa kishin ƙasa a sahun gaba,” cewar Idris.

Ministan ya ƙara da cewa, tasirin kishin ƙasa da aiki da gaskiya, Tinubu ke ta faɗi-tashin cusawa da kwaɗaitarwa.

“Ya ba mu umarni kai-tsaye cewa, mu tabbatar waɗannan kyawawan ɗabi’u da halaye nagari sun kasance jigo a ƙoƙarin faɗakar da mafi yawancin ‘yan Nijeriya.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here