Babu ranar da ba a hallaka mutane a Katsina – Radda

0
160

Gwamnan jihar Katsina, Umaru Dikko Radda ya ce babu ranar da za a wayi gari ba tare da samun labarin kisan mutane ba a faɗin jihar sanadiyyar matsalar tsaro.

Gwamnan ya faɗi haka ne yau Alhamis lokacin wata tattaunawa da manema labaru a Abuja.

Gwamnan ya ce matsalar tsaro ta yi wa jihar katutu, ta yadda ƴan fashi a kowace rana ke kai hare-hare a ƙauyukan jihar suna kisa da garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

A cewarsa “Babu ranar da zan tashi ba tare da samun labarin kisan mutane ba a jihata, har tsoron kunna wayata nake ji saboda na san labarin da zan samu ke nan.”

Gwamnan ya ce a kan haka ne ya tara ƙwararru waɗanda suka zauna tare da fito da tsarin kafa yan sintiri na jiha, waɗanda za su taimaka wajen samar da tsaro a yankunansu.

Katsina na cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro ta ƴan fashin daji waɗanda suka kwashe shekaru suna kai hare-hare a ƙauyuka da garuruwan jihohin.

Gwamnatin Tarayya dai ta kaddamar da shirye-shiryen soji da dama a yankin domin yaƙi da matsalar, sai dai har yanzu lamarin na ƙara kazancewa.

Gwamnan na Katsina ya ce idan samar da tsaro ne kaɗai aikin da zai yi a tsawon wa’adin mulkinsa, ya shirya yin hakan.

Ya bayyana cewa tun kafin zamansa gwamna, ya zagaya faɗin jihar inda ya ga yadda al’umma ke cikin uƙuba sanadiyyar rashin tsaro.

Gwamnan ya kuma ce a yanzu an fara samun ingantuwar tsaro a jihar bayan kaddamar da rundunar ‘yan sintiri ta jihar.

Ya ce “a yanzu bayan kaddamar da rundunar sintiri na yi kwana biyu ba tare da na samu labarin kisan mutane ba a Katsina.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here