Motar gidan yari ta afka kan ‘yan kasuwa a Kwara

0
133

Akalla mutum biyu aka ruwaito sun rasa rayukansu a yayin da motar bas ta gidan gyaran ta kwace wa direbanta, ta kutsa cikin masu sayar da kaya da wajen da masu sana’ar acaba ke tsayawa a yankin Ojo-Oba a Ilorin da ke a jihar Kwara.

Hatsarin wanda ya auku a ranar Alhamis, ya auku ne bayan da direban motar ya dauko wasu da ake zargi masu laifi ne da za a kai kotu, wanda hakan ya kuma janyo mutane da dama suka jikkata.

Wani ganau ya ce, direban wanda ya taho a guje, ba hannunsa ya biyo ba kuma a lokacin yana tukin yana buga waya.

Kazalika, motar ta kade wani dan achaba daya ya rasu daura da titin Neja a lokacin da direban ke kokarin tserewa da wasu mutane da suka farmake shi.

Wata mai sayar da abinci mai suna Hajara ta ce, motar ta kade ‘ya’yanta biyu sun samu raunuka wadanda aka garzaya da su zuwa asibiti don yi musu magani.

Kakakin rundunar ‘yansandan jihar Kwara Ajayi Okasanmi, ya tabbatar da aukuwar hatsarin, sai dai ya ce, babu wanda ya rasu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here