Hukumar kula da gidajen yari ta yi wa fursunoni 1,137 rajistar NECO a Enugu

0
165

Hukumar Kula da Gidajen Yarin Najeriya ta ce ta yi wa fursunoni 1,137 rajista domin shiga jarrabawar kammala makarantar sakandare ta ƙasa (NECO) a jihar Enugu.

Hukumar ta ce ta yi wa’ ɗaurarrun rajistar ne cikin shekara 12 da suka gabata.

Jaridar Punch a Nariya, ta ruwaito Kwanturolan gidan yarin Enugu, Nicholas Obiako na bayyana cewa a halin yanzu fursunoni 124 ne ke zana jarabawar NECO da ke gudana a cibiyar rubuta jarrabawar a jihar ta bana a jihar.

Ya kara da cewa ”ci gaban karatun fursunonin ya fara ne tun daga azuzuwan firamare da sakandare zuwa ingantaccen ilimin manya, yana inganta dogaro da kai da kare lafiyar jama’a bayan zamansu a gidan yari”.

Bugu da kari, ana ba da horon sana’o’i a fannoni kamar ɗinki, aikin ƙarfe, da na katako, wanda ke ba da gudummawa ga gyare-gyaren halayen fursunonin domin sake shiga cikin jama’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here