Kotun daukaka kara ta ayyana ranar yanke hukunci kan kujerar gwamnan Adamawa

0
211

Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta sanar da ranar 1 ga watan Disamba a matsayin ranar da za ta yanke hukunci kan karar da Sanata Aishatu Dahiru Ahmad Binani, ta shigar.

Binani, ta daukaka kara ne kan hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke na tabbatar da Gwamna Ahmad fintiri a matsayin halastaccen gwamnan jihar Adamawa.

A’ishatu Binani ‘yar takarar gwamna ce a jam’iyyar APC inda ta gwabza da gwamna Ahamd Fintiri na jam’iyyar PDP a zaben da ya gudana a watan mayun 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here