Kujeru 300 kawai muka sayar daga cikin 6,000 da aka ware wa Kano — Hukumar Alhazai

0
294

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano ta nuna damuwarta bisa ga yadda ake samun jinkiri wajen sayar da kujerun aikin Hajjin bana a jihar, duba da cewa a yanzu haka kujeru 300 kacal daga cikin 6,000 da aka tanadar domin maniyyatan jihar ta sayar.

Shugaban Hukumar, Alhaji Laminu Rabiu Danbappa ne ya bayyana haka a yayin da yake zantawa da jaridar Aminiya a Kano.

Danbappa ya ce Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta sanya ranar 5 ga watan Janairu a matsayin ranar da za ta rufe rajistar maniyyata da karbar kudaden aikin Hajjin bana daga jihohin kasar.

Ya ce din haka akwai buktar maniyyatan jihar da su biya kudin kafin-alkalami kafin ranar 25 ga watan Disamba, 2023.

Danbappa ya kara da cewa Kasar Saudiyya ta bayyana cewa za ta kammala aikin bayar da biza ga maniyyatan kwana 50 kafin ranar Arfa.

‘“Kasancewar Saudiyya ta bayar da wa’adin cewa za ta rufe bayar da biza kwana 50 kafin ranar Arfa wanda kuma daga haka babu wani taimako da za m iya yi wa maniyyaci matukar Saudiyyar ta rufe yin bizar.

“Kan haka ne muke kokarin mu yi duk abin da ya dace a kan lokaci domin gujewa abin da kin yin hakan ka iya jawo wa maniyyaci.”

Ya yi kira ga jami’an Hukumar Alhazai na kananan hukumomin jihar da su rubanya kokarinsu wajen sayar da kujerun da aka ba kowacce karamar hukuma a kan lokaci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here