Dumamar yanayi ta haddasa ruwan saman ba-zata a Arewa – NiMet

0
175

Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta bayyana cewa sakamakon dumamar yanayi ne ta haddasa ruwan sama a wasu sassan arewacin Nijeriya a karshen makon da ya gabata zuwa farkon makon nan.

A cewarta, wannan na kara tabbatar da irin illar da gurbacewar sararin samaniya ke haifarwa, kuma ya zama dole a hada hannun wajen rage dumamar yanayi ta hanyar rage yadda iskar ‘carbon diodide’ ke gurbata muhalli.

Hukumar ta bayyana hakan ne a wajen wani taron kara wa juna sani da ta shirya wa ‘yan jarida tare da hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniy na, wajen tunatar da ‘yan jarida kan dumamar yanayi ta yadda za su fadakar da al’ummar kasar nan.

Taron ya gudana ne a Otel din Rock Biew da ke Abuja, inda ta ce wannan wani sharar fage ne kan babban taron da aka fara a kasar Dubai daga ranar 30 ga Nuwamba zuwa 12 ga Disamba.

Hukumar NiMet ta yi nemi ‘yan jarida su kara kaimin fadakar da al’ummar Najeriya kan illar dumamar yanayi a bangaren lafiya da tattalin arziki da kuma yadda za a magance matsalolin ta hanyar da ta dace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here