Hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Gaza laifi ne na cin zalin bil’adama – Erdogan

0
198
Erdogan
Erdogan

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Gaza a matsayin “laifi na yaƙi da cin zarafin bil’adama.” 

“Abin da ke faruwa a Gaza laifi ne na yaƙi, laifin cin zarafin bil’adama ne. 

Dole ne a hukunta wadanda suka aikata irin wadannan laifuka a karkashin dokokin kasa da kasa,” in ji Shugaba Erdogan a jawabin da ya gabatar a wajen taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya na shekara ta 2023 a birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, (UAE) a ranar Juma’a. 

A hare-haren da Isra’ila ta kai ta kashe Falasdinawa sama da 16,000, yawancinsu mata da kananan yara, kuma ba ta da wata hujja ta kare kanta a aikata hakan, in ji Erdogan. 

Ya kara da cewa, Turkiyya na tsayawa tsayin daka wajen tabbatar da zaman lafiya a duk cikin rikice-rikicen da ake fama da su, kuma tana kokarin samar da mafita mai adalci. 

Da sanyin safiyar Juma’a ne Isra’ila ta ci gaba da kai hare-haren soji kan Zirin Gaza bayan kawo karshen tsagaita wuta, inda ta kai hare-hare a yankuna daban-daban a arewaci, da tsakiya, da kuma kudancin yankin da aka yi wa ƙawanya, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da jikkata wasu, a cewar ma’aikatar a Gaza.

Akalla Falasdinawa 32 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata yayin da Isra’ila ta sake kai hare-hare a yankunan Gaza cikin sa’o’i da kawo karshen tsagaita wutar, in ji ma’aikatar. 

A safiyar Juma’a ne dai aka kawo karshen tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas wanda ya fara aiki a ranar 24 ga watan Nuwamba. 

Taron Ƙoli kan Yanayi na Majalisar Dinkin Duniya na 2023, wanda aka fi sani da COP28, ya samu halartar shugabannin kasashe da gwamnatoci sama da 180 daga sassan duniya. 

Wani abin lura shi ne yadda ya samu bukatar masu son halarta inda yawan mahakartan ya 500,000.

Za a ci gaba da taron har zuwa ranar 12 ga watan Disamba. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here