Khadijah Mai Numfashi ta nemi afuwa bayan dakatar da ita daga Kannywood

0
169

Jarumar Kannywood Khadija Kabir Ahmad wadda aka fi sani da Mai Numfashi, ta tuba bayan Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta dakatar na tsawon shekara biyu.

Khadija Mainumfashi ta bayyana tubar tata ce ta wani bidiyo da ta sanya a shafinta an TikTok, kasa da kwana 10 da shugaban hukumar, Abba Al-Mustapha ya sanar da haramta mata shiga duk harkokin Kannywood.

Hukumar ta dakatar da Khadija Mainumfashi ne kan wani bidiyon rawar Solo da jarumar ta yi a wani gidan Gala, wanda ya jawo ce-ce-ku-ce.

A bidiyo da ta wallafa ranar Alhamis, Mainumfashi ta nemi afuwar Hukumar da duk wadanda bidiyon bai yi ya dadi ba, tana mai cewa ita kanta ba ta ji dadin abubuwan da ta aikata ba a bidiyon rawan.

“Ina kara ba wa hukumar tace fina-finai hakuri sannan ina kara ba wa masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood hakuri, da daukacin al’umma Annabi Muhammadu (SAW) da ba su ji dalin bidiyon ba.

“Ni kaina ban ji dadinsa ba, ina mai kara ba ku hakuri, a yi hakuri in sha’a Allahu hakan ba zai kara faruwa ba,” in ji jarumar.

Bidiyon nata da ya sa aka dakatar da ita, ya fito ne a daidai lokacin da ake ce-ce-ku-je bayan daraktan Kannywood, Abdallah Amdaz ya zargi wasu daraktoci da furodusoshi da lalata da jarumai mata kafin su sa su a fim.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here