CBN zai haramta amfani da asusun bankin da babu BVN da NIN a 2024

0
205
CBN

Babban bankin Nijeriya (CBN), ya sanar da matakin haramta hada-hadar kudi a asusun ajiyar banki da babu BVN da lambar NIN daga watan Maris din 2024.

A wata takardar da aka raba wa bankunan kasuwanci da sauran cibiyoyin kudi da masu gudanar da hada-hadar kudi, CBN ya ce za a hana amfani da asusun ajiyar

Babban bankin ya yi gargadin cewa dole ne asusu ya zamana yana da BVN ko NIN.

CBN ya ce nan ba da dadewa ba za a gudanar da cikakken bincike kan asusun da babu BVN ko NIN, kuma da zarar an samu babu za a dakatar da asusun.

“Dukkan cibiyoyin hada-hadar kudi da CBN ke jagoranta ana bukatar su yi aiki da tsauraran matakai kan takunkumi kan asusun ajiya,” in ji Efobi da Mustapha a cikin takardar sanarwar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here