Muna fuskantar cin zarafi daga sojoji – ‘Yan ‘uwan Bazoum

0
180
Bazoum
Bazoum

Sanarwar da ‘yan ‘uwan nasa suka fitar, ta ce, tun daga ranar 18 ga Oktoba, ba a kara jin duriyar Bazoum, matarsa Khadija Mabrouk tare da dan su salem ba.

Tun daga lokacin da aka hambarar da shi a ranar 26 ga watan Yuli, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi, Mohammed Bazoum ya ci gaba da kasancewa a tsare a fadar shugabancin kasar tare da mai dakinsa da kuma dansu.

Sanarwar da aka mikawa AFP, ta ce da dama daga cikin ‘yan ‘uwan hambararren shugaban suna fuskantar cin zarafi, wasu kuma an cafke su, yayin da wasu kuma sojoji ke neman su ruwa a jallo.

A cewar lauyan ‘yan ‘uwan nasa, sojoji sun kai samame gidan ‘yar ‘uwar Mohammaed Bazoum da kuma wasu na daban da ke birnin Yamai a ranar Talata.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, a anar Lahadi ne, wasu mutane dauke da bindigogi suka yi awun gaba da Ali Bey Mahjoub, wanda ya kasance babban ma’aikacin banki kuma dan ‘uwa ga Bazoum.

Haka zalika a ranar 9 ga Nuwamba, wani basarake da ya kasance dan ‘uwa g amai dakin Bazoum, shima jami’an jandarma suka yi awun gaba da shi a Zinder, inda har yanzu yake tsare a hannun ‘yan sanda, kamar yadda lauyansa ya tabbatar.

Nijar dai na karkashin mulkin soji tun ranar 26 ga Yuli, inda Janar Abdourahamane Tiani, yam aye gurbin Bazoum bayan juyin mulkin da ya hambarar da shi kan karagar mulki.

Bayanai sun tabbatar da cewa, tun daga lokacin ake ci gaba da kame ko kuma tsare manyan jami’an gwamnati, kama da ministoci a gidajen yari da ke sassan kasar.

Bayan juyin mulkin ne, kungiyar raya tattalin arzkin kasashen Yammacin Afirka, ECOWAS, ta yi barazanar amfani da karfin soji wajen dawo da Bazoum kan mukaminsa, tare da sanya takunkumin tattalin arziki kan kasar.

RFI

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here