Diyyar rusau: Kotu ta ba da umarnin kulle asusun gwamnatin jihar Kano 

0
171

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta bayar da umarnin dakatar da harkokin asusun gwamnatin jihar Kano a bankunan kasuwanci 20 da wasu asusu 4 a Najeriya.

Mai shari’a I.E Ekwo ya bayar da wannan umarni ne a wata kara da masu shagunan massalacin Idi da kungiyar ‘yan kasuwa suka shigar a kan ruguza shagunansu wanda suka bayyana a matsayin haramtaccen mataki da jihar ta dauka a watan Yunin 2023.

Dailynews24 ta ruwaito cewa wadanda suka shigar da karar, Alhaji Awalu sai’du, Ifeanyi Nwobodo, Alhaji Sani Uba, Alhaji Abdullahi A. Idris, da wasu mutane 25 sun kai karar gwamnatin jihar Kano, a matsayin masu bin doka da oda inda suka nemi diyyar N30bn.

Umurnin yana kunshe ne a cikin (CTC) na hukuncin da aka bayar a ranar 28 ga Nuwamba, 2023 kuma aka bai wa manema labarai a ranar Laraba.

A cewar CTC, Asusun bankunan da za’a kulle sune CBN, FAAC, Asusun jihar na tarayya da kuma bankunan kasuwanci da suka hada da UBA, Access, Jaiz, TAJ, Union, Keystone, da wasu guda 17, kotun ta yanke wannan hukuncin ne sakamakon kin biyyan diyyar N30bn da ta ayyana akan gwamnatin jihar.

Umarnin ya dakatar da duk wasu kudade na gwamnatin jihar Kano da zasu shiga cikin wadannan asusun a yanzu ko anan gaba.

Har ila yau, ta ba da umarnin tarar data ci gwamnatin Kano a biya a gaban wannan kotu mai daraja, Kotun takara da cewar wannan ya biyo bayan wani kudiri ne da aka shigar a ranar 10 ga Oktoba, 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here