RAHOTO: Masu cutar asma na iya karuwa a Kano, yayin da farashin abun shaka ke kara tsada 

0
207

Masu fama da lalurar Asma sun koka kan tsefewar farashin kudin magungunan cutar musanman abun shaka (Inhaler) dake zame musu garkuwa ga cutar a duk lokacin da ta taso musu.

Kokawar na zuwa ne dai-dai lokacin da yanayin sanyi ke kara tunkarowa, kuma masana kiwon lafiya sun tabbatar cewa a lokutan hunturu, masu fama da lalurar Asma na mutukar shan wahala la’akari da kura dama wasu ababen dake sabbaba tashin cutar.

Binciken Jaridar Dailynews24 data gudanar kan shagunan sayar da magunguna a cikin kwarya birnin Kano, ta gano cewa an samu tsefewar farashin gwan-gwanin maganin cutar da ake yiwa lakabi da Inhaler. 

Guda daga cikin Shagunan sayar da Mugungunan mai lakabin NOVOMED dake Jihar Kanon sun tabbatarwa da wakilan Jaridar Dailynews24 suna sayar da kwalbar kan farashin Naira Dubu Sha Uku da Dari Hudu a ranar 4 ga watan Disambar shekarar 2023. 

Kazalika, binciken Jaridar Dailynews24 ta kuma tuntubi Shagon sayar da Magunguna na LAMCO inda guda daga cikin ma’aikatansu ya bayar da farashin kan Naira Dubu takwas, inda sauran shagunan magunguna da Jaridar ta bincika sun ki amincewa da bukatar sanin farashin har sai sun ga shaidar likita.

Hajiya Fatima Sagir Ahmad, guda ce cikin mutane Miliyan Sha Uku dake fama da cutar Asma a Najeriya ta labarta wa Jaridar Dailynews24 cewa an samu rubunyawar farashin kwalbar Inhaler inda wasu lokutan akan samu karancin sa.

“Kamar wattanin 8 da suka gabata, muna sayen kwalbar Inhaler kan Naira Dubu Guda da Dari Bakwai domin sayen Kwalbar Inhaler nau’in Ventoline ko Seretide, kwatsam muka ji cewa farashin ya tashi zuwa Naira Dubu Sha Takwas da Dari Biyar, har inka samu kenan” Itama, Halima Aliyu wata matashiya ce mai fama da cutar Asma ta tabbatar da ikirarin da Hajiya Fatima Sagir Ahmad ga Jaridar Dailynews24 cewa a farkon shekarar 2023, tana sayen kwalbar Inhaler kan Naira Dubu Guda da Dari Bakwai.

Dakta Hasana Abubakar Imam, kwararriya kan cutar Asma a asibitin Koyarwa na Malan Aminu Kano dake Jihar Kano ta labarta wa Jaridar Dailynews24 cewa ficewar wani kanfanin kasa da kasa da ake kira GlaxoSmithKline daga Najeriya ne ya sabbaba tsefewar farashin da karancin Inhaler. 

Sai dai binciken Jaridar Dailynews24  Kanfanin ya fice ne biyo bayan cinkaro da matsalar samun Dalar Amurka domin sayen kayayyakin hada maganguna daga kasashen ketare. 

Bukatar magungunan Asma na karuwa inda samuwarsa ke raguwa inda hakan ke kara ta’azzara tsefewar farashin magungunan inda hakan ke sabbaba gaza sayen magangunan ga masu fama da cutar.

Duk da cewa bata tabbatar da cewa an samu karuwar masu fama da cutar Asma zuwa asibiti ba, amman ta tabbatar da cewa ficewar Kanfanin GlaxoSmithKline daga Najeriya ya haifar da matsala, musanman kasancewar Najeriya kan gaba wajen yawan mutanen dake fama da cutar a nahiyar Afrika.

Harwayau, wasu majiyoyin kafafen yada labarai sun tabbatar da cewa tsefewar farashin magunguna a Najeriya na haifar da tsadar rayuwa dake zama ruwan dare a Najeiya da sauran kasashen duniya.

Masana harkokin magunguna ta fuskar tattalin arziki, sun ce tsefewar farashin kiwon lafiya a kasashen duniya na tilastawa marasa lafiya neman wata hanyar da ya sabawa ka’idar neman lafiya a zamanance.  

Rahoton: Abdussamad Muhammad Usman da  Aisha Aliyu Zubairu Dailynews24    

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here