Yadda karancin masu bayar da tallafin jini ke barazana ga rayukan ‘yan Najeriya – Dakta Gwarzo

0
180

Abdussamad Muhammad Usman

Dakta Dalhatu Halilu Gwarzo Guda daya daga cikin masanan kiwon lafiya ta fuskar jini a Najeriya, ya koka kan yadda masu bayar da jinin fisabillilahi a Najeriya ke kara karanci tare da bayyana yadda karancinsu ke barazana ga dubannin rayukan masu fama da cutukan dake da alaka ta da tallafin jini.

A wata zantawa ta musamman da jaridar Hausa24, Dakta Gwarzo wanda kwararre ne a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano dake Jihar Kano, yace ana samun ledar jini 500,000 maimakon leda 1,800,000 a kowwace shekara, adadin dake gaza abinda fannin kiwon lafiyar kasar ke bukata a cewar masana.

Acewar Dakta Dalhatu Halilu Gwarzo, Hukumar Lafiya ta Duniya ta alakanta gazawar samun adadin da karancin masu bayar da tallafin Jini Fisabilillah a Najeriya ne.

“Munada nau’ikan masu bayar da jini uku ne a cewar  Dakta Dalhatu Halliru Gwarzo a lokacin da yake zantawa da Jaridar Hausa24”.

A wani rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya WHO na shekarar 2023, hukumar ta haska cewa Kasashen Afrika sune suka fi karancin masu bayar da gudunmuwar Jini duk da cewa sune ke kan gaba wajen cin gajiyar hakan.

“A kasashe masu tasowa, kiddidiga ta nuna cewa kaso 90% na  gudumuwar jini na zuwa ne daga dangin da iyalen masu bukatarsa inda binciken ya kuma yi nuni da cewa kaso 10% ne suke bayar da tallafin jini Fisabillillahi a Najeriya a cewar Rahoton WHO”.

Dakta Gwarzo ya kuma zayyana rukunin mutane da suka fi samun kansu cikin halin bukatar tallafin jini, sun hada da Masu fama da Amosanin Jini, Mata masu Juna biyu kafin da gabbanin haihuwa, wadanda hadarin mota ya rutsa dasu inda Najeriya na kan gaba wajen yawan masu fama da cutar Amosanin Jini a fadin duniya.

“Akwai masu lalura dayawa dake bukatar gudunmuwar Jini. misali, masu cutar Amosanin Jini, Cutar Koda, mata masu juna biyu  gabbanin da bayan haihuwa, wadanda hadari ya rutsa dasu dama masu fama da cutar daji dake cigaba da karuwa a Najeriya a cewar Dakta Gwarzo”

Dakta Gwarzo ya yi jan hankali kan yadda ake asarar rayuka da samu nakasu biyo bayan gazawar samun adadin ledar jinin da ake bukata a Najeriya.

Kazalika, wani rahoton Shirin Muradun Karni dake yiwa lakbi da Sustainable Development Goals ya yi nuni da cewa mata masu juna biyu akalla 1,047 ne ke rasa rayukansu a duk cikin mata 100,000 da suka je haihuwa biyo bayan rashin wadattacen jini, kuma Najeriya ce ta uku baya ga kasar Sudan ta Kudu da Kasar Chadi.

Wani bincike na baya-bayannan ya yi nuni da cewa mata masu juna biyu na kan gaba wajen bukatar jini a Jihar Kano a cewar Dakta Gwarzo na Asibitin Koyarwa na Malan Aminu Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here