Kin tantance takardun shaidar karatun Benin da Togo zai shafi dalibai 15,000 – NANS

0
180
Togo

Ƙungiyar Ɗaliban Najeriya ta NANS, reshen ƙasar Benin ta yi kira ga hukumomin Najeriya da su sassauta dokar soke tantance takardun shaidar karatun digiri daga ƙasashen Benin da Togo,

Shugaban ƙungiyar NANS reshen ƙasar Benin Ugochukwu Favour ne ya yi wannan kira a lokacin wata tattaunawa da yi da kafar yaɗa labarai ta Channels ranar Alhamis.

Yana mai cewa matakin zai shafi ɗaliban Najeriya 15,000 da ke karatu yanzu haka a ƙasar ta Benin.

A farkon makon nan ne wani ɗan jaridar Daily Nigerian ya bayyana yadda ya samu digirin boge cikin mako shida a wata jami’a da ke ƙasar ta Benin har ma ya samu damar shiga sansanin ‘yan yi wa ƙasa hidima.

Bayan ɓullar rahoton ne gwamnatin Najeriya ta fitar da sanarwar dakatar da tantance takardun shaidar digiri daga ƙasashen Benin da Togo.

To sai dai shugaban ƙungiyar ɗalibana Nejeriya NANS, reshen ƙasar Benin ya ce ya kamata gwamnati ta yi la’akari da ɗaliban da suka samu gurbin karatu kuma suke karatun ta hanyar da ta dace.

“Abin da zan ce shi ne, ya kamata gwamnatin tarayya ta duba lamarin, babu yadda za a yi don abu ya faru a wata makaranta, sannan a yi hukuncin da zai shafi kowa, saboda matakin ya shafi ɗalibai kusan 15,000 da ke karatu a Benin”.

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here