‘Na fi jin dadin rawar da na taka a matsayin Mainasara a shirin Labarina’ – Sadiq Sani Sadiq

0
141
Sadiq Sani Sadiq
Sadiq Sani Sadiq

A wata tattaunawa da akayi da fitacen Jarumin na Kannywood wato Sadiq Sani Sadiq a Gidan Jaridar TRT ya bayyana wasu sirrika da suka shafi Labarina.


Inda acikin tattaunawar aka tambaye shi, tsakanin Jamila da Maryam acikin shirin labarina waye yafi jin dadin aiki da ita?


Jarumin yace “A gaskiya dukkansu biyun yana jin dadin aiki dasu, inda yace duk da cewa Ita Maryam ba wannan ne farko aikin su ba, amma yanayin aikin da suka yi da ita a Labarina dukkansu biyun sun burge shi.


Inda ya kara da cewa Kowacce ta taka rawar da yakamata ta taka a rubuce harma da kari sun kakkara wajen yin kokari. Inda ya kara jaddada cewa Gaskiya dukkansu yaji dadin aiki dasu sosai.


An sake tambayar Jarumi Sadiq Sani Sadiq akan “Shin akwai wani banbanci tsakanin Role din da ya taka a matsayin Al’amin da sauran Role da yake takawa?


Jarumi Sadiq Sani Sadiq yace “ E to ba zai ce akwai wani bambanci ba acikin rawar da ya taka a matsayin Al’amin acikin Labarina da kuma sauran Fina-finai da nake yi. Sai dai kawai fitowa a matsayin Al’amin shiri ne mai dogon zango ba irin fim din da muka saba yi bane.


Sannan shi Al’amin wani mutum ne da ya boye kamarsa ya mayar da kansa Talaka Dan tasha saboda ya cimma wani burinsa. Sannan kuma yakan sauya daga wannan yanayin zuwa wani yanayi, shine kawai bambancinsa da sauran fina-finan da ya saba yi.


An tambaye shi “Ya batun kalubale da ya fuskanta lokacin da aka soma sakin Shirin Labarina na Takwas?


Sadik Sani Sadik yace “Babu wani Kalubale da ya fuskanta!


Menene Bambancin Al’amin na Tasha da kuma lokacin da ya bayyana a matsayin Mainasara?


Jarumi Sadik Sani Sadik yace yafi jin dadin lokacin da ya bayyana a matsayin mai kudi fiye da Dan tasha, Domin role din Matashin mai kudi ne Mai nasara, yadda ya gabatar da kansa, yanayin maganarsa da tafiyarsa yadda ya sauya.


Wani Sin ne kafi so a cikin shirin Labarina?


Sin din da jarumin ya bayyana shine lokacin da Iyalinsa suka mutu yazo asibiti yaga gawawwakinsu, yanayin da ya shiga a wannan lokacin hatta wadanda suke kallo da Ma’aikatan da suke aiki dasu kowa sai da ya tausaya masa a wannan lokacin. Ya kuma bayyana cewa ya dade bai samu kiraye-kiraye da suka kai irin wannan lokaci da yake wannan shiri ba sannan ya bayyana cewa wasu Masoyansa ma har mantawa suke da Sunansa na asali inda suke kiransa da Al’amin ko Mainasara.


Wani albishir zaka yiwa masu kallon Labarina?


Sadiq Sani Sadiq yace su dage su cigaba da kallon fim din Labarina saboda akwai abubuwa da yawa anan gaba. Wadanda sakonni ne kuma nishadantarwa ne, A karshe kuma yace Yana iya cewa yanzu ma aka fara ko kuma yace bama a fara ba, sannan akwai abubuwan da zasu sa mutane Kuka da Nishadi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here