Hadiza Gabon ta yi martani ga masu magana kan ramarta

1
128
Hadiza Gabon
Hadiza Gabon

Jarumar masana’antar kannywood Hadiza Aliyu wacce aka fi sani da Hadiza Gabon ta bukaci masu magana akan ramar da tayi a kafafen Sada Zumunta da su mai da hankali akan abun da ya dami Arewacin Najeriya da Kasa baki daya.

” Me yasa yan Arewa bama mai da hankali kan matsalolin da suka dame mu ne”.

Hadiza Gabon ta bayyana hakan ne a sahihin shafinsa na Facebook.

A shafin nata Hadiza Gabon ta goyi bayan duk mutanen da suka kalubanci masu ganin baiken ramar ta ta, mai makon mai da hankali kan matsalolin tsaro da talauci da tsadar abinchi da suke addabar al’ummar Nigeria.

A yan makwannin nan an ga hotunan yadda Jarumar ta rame sabanin yadda aka santa da gibarta. wasu suna ta hasashen cewa maganin rage kina jarumar ta sha, don rage kibarta.

Sai dai mutane da yawa suna ganin kamata yayi masu surutu akan batun su mai da hankali wajen yin kiraye-kirayen a magance matsalolin da suka addabi arewa.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here