Kano: Likitoci sun dakatar da ayyukansu a Asibitin Murtala

0
158
Asibitin Murtala

Kungiyar Likitoci ta Najeriya, NMA ta sanar da matakin janye ayyukanta a asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano har sai yanda hali ya yi bayan da wasu da ta kira ‘fusatattun mutane dauke da makamai’ suka far wa wani likita da ke bakin aiki.

Kungiyar ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da sakatarenta ya fitar ranar Lahadi inda ta ce yan’uwan wata mata da ke jinya ne suka tayar da hatsaniya inda suka boye likitan sai dai daga bisani mahaifin likitan, wanda shi ma yake aiki a asibitin ya samu kubutar da ɗansa.

Zuwa yanzu, BBC ba ta kai ga tantance abin da ya sa mutanen suka far wa likitan ba.

Kungiyar ta ce shugabanninta sun je wajen da lamarin ya faru inda suka lura cewa akwai rashin isasshen tsaro a asibitin abin da ta ce babban kalubale ne ga ma’aikatan lafiya da ke aiki a asibitin.

Sakataren kungiyar ta NMA ya ce dalilin haka ne ya zama dole kungiyar ta janye mambobinta daga aiki cikin yanayi na rashin tabbas har sai hukumomin asibitin sun tabbatar masu da tsaro.

A cewar kungiyar, za su ci gaba da bibiyar yanayin tare da shawartar mambobinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here