Rarara ya gwangwaje Tijjani Asase da kyautar gida da N1m

0
604

Shahararren mawakin siyasa dake Arewacin najeriya Dauda Adamu Kahutu Rarara ya gwangwaje shahararren jarumin wasan Hausa wato Tijjani Asase da kyautar Gida da Naira miliyan daya.

Kwana uku zuwa hudu da fara daukar shirin Matar Mutum biyu kashi na 2 wanda jarumin wato Tijjani Asase yake ciki, wanda ake daukar shirin a unguwar Rijiyar zaki, kwatsam sai labari ya ishe shi tare da bashi takardun gidan da aka yi masa kyautar sa. 

Dama Jarumi Tijjani Asase ya kasance masoyi kuma na hannun dama agurin Fitaccen Mawakin siyasar.

Ko a kwanakin baya ma mawakin ya gwangwaje jarumin Tijjani Asase da kyautar mota, inda jarumin ya wallafa tare da nuna godiyarsa ga mawakin. A wannan karo ma ya sake wallafa wani bidiyon. Inda a bidiyon ya bayyana farin cikinsa tare da abokan sana’ar tasa da suke daukar shirin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here