AFCON 2024: Afrika ta kudu za ta fafata da Cape Verde bayan fitar da Morocco

0
131
Afrika ta kudu
Afrika ta kudu

Afrika ta kudu ta fitar da Morocco daga gasar cin kofin Afrika a wasan da suka doka tsakaninsu daren jiya Talata wanda ya bai wa Bafana Bafana damar tsallakawa zuwa matakin wasan gab da na kusa da karshe da za ta hadu da Cape Verde.

Achraf Hakimi ya barar da bugun fenaritin da ya samu a minti na 85 wadda ke matsayin dama daya tal ga Morocco ta farke kwallon da Bafana Bafana ta zura mata a minti na 57 ta hannun Evidence Makgopa.

Morocco ta kammala karawar da ‘yan wasa 10 bayan korar Sofyan Amrabat daga fili a minti na 94 sakamakon ketar da ya yi wa Mokoena.

An dai yi gwagwarmaya a haduwar ta jiya kamar yadda aka yi tsammani domin sai bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne Bafana Bafana ta iya zura kwallon gabanin kara ta biyu a minti na 95.

Yanzu haka dai Afrika ta kudu wadda ta lashe kofin gasar a 1996 ta kama hanyar maimaita tarihi, sai dai haduwarta da Cape Verde ranar Asabar ne zai tabbatar da ko za ta iya ci gaba da kasancewa a gasar ko akasin haka.

Tawagar ta Atlas Lion wadda ta kai wasan gab da karshe na gasar cin kofin Duniya a bara, na matsayin ta 1 ne a matakin iya kwallo a Afrika kuma rabonta da lashe kofin tun shekarar 1976, yayinda kasar ke shirin karbar bakoncin makamanciyar gasar ta 2025.

Morocco dai ta yi wasan na jiya ba tare da Hakim Ziyech da Sofiane Boufal ba wadanda ake ganin rashinsu ya hadddasawa tawagar koma baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here