AFCON 2024: Yadda fafatawar kasashe 8 za ta gudana

0
148
AFCON 2024

A gobe Juma’a ne ake shirin fara doka wasannin zagayen gab da na kusa da na karshe na gasar cin kofin Afrika da ke ci gaba da gudana a Ivory Coast, wasannin da za a fafata tsakanin kungiyoyi 8 da suka tsallake daga matakin ‘yan 16.

A goben dai za a faro ne da wasa tsakanin Najeriya da Angola wanda zai gudana da misalin karfe 6 na yammaci a filin wasa na Houphouet-Boigny da ke birnin Abidjan.

Sa’o’I 3 bayan shi wannan wasa ne kuma za a hadu tsakanin DR Congo da Guinea da misalin karfe 9 na dare a filin wasa na Alassane Ouattara duk dai a birnin na Abidjan.

Wasannin za su ci gaba a ranar Asabar inda za a hadu tsakanin Mali da mai masaukin baki Ivory Coast da misalin karfe 6 na yamma a filin wasa na Stade de la Paix da ke birnin Bouake.

Itama Cape Verde za ta hadu da Afrika ta kudu ne da misalin karfe 9 na dare fafatawar da za a yi a filin wasa na Yamoussoukro da ake kira Charles Konan Banny.

Wani abu mai bayar da mamaki a gasar ta AFCON a bana shi ne yadda aka yi waje da ilahirin kasashen da suka kai irin wannan mataki a magabaciyar gasar ta 2019.

Za dai a karkare wasannin gasar ta AFCON tare da fitar da wadda ta yi nasara tsakanin kasashen a ranar 11 ga watan Fabarairun nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here