AFCON 2024: Zamu canza salon wasanmu yayin karawa da Najeriya – Kocin Afirika Ta Kudu

0
103

Mai horas da tawagar ‘yan wasan kasar Afirika Ta Kudu, Hugo Bruce, ya bayyana cewar yan wasansa za su canza salon yadda suke taka leda a wasan da za su kara da Najeriya a ranar Laraba.

Hugo wanda ya tabbatar da cewa Najeriya ba kanwar lasa bace duba da inda suka fito da kuma yadda suke taka leda da jajircewa a dukkan wasannin da suka buga a gasar AFCON ta bana.

Bayan shafe shekaru 24, kasar Afirika Ta Kudu ta samu nasarar tsallakawa zuwa matakin na kusa da na karshe a gasar AFCON inda za ta hadu da Najeriya.

A karshe Bruce ya ce duk da ya yarda da yanayin yadda yan wasansa ke taka leda, ba za su dauki karawa da Najeriya da wasa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here