An katse hanyoyin intanet a Senegal bayan barkewar zanga-zanga

0
87
Senegal

Gwamnatin Senegal ta sanar da katse hanyoyin intanet na wani dan lokaci a kasar, kwana daya bayan daruruwan mutane sun yi zanga-zangar adawa da matakin Shugaba Macky Sall na dage zaben shugaban kasa.

Gwamnatin ta ce matakin ya zama dole domin dakatar da yada sakonnin kiyayya da na tada rikici a shafukan sada zumunta kam,ar yadda ministan sadarwa, Moussa Bocar Thiam ya fada.

Lamarin ya zo kwana daya bayan da yan Senegal suka far wa wani gidan Talabijin kan zargin yana tada husuma a yadda yake bayar da rahotanni kan zanga-zangar.

A yau ne yan majalisar kasar za su tafka muhawara kan wani kuduri da ke ba da shawarar a yi zaben shugaban kasa ranar 25 ga watan Agusta tare da kyale Shugaba Sall kan kujerarsa har sai an samu magajinsa. Tun farko an tsara yin zaben a ranar 25 ga watan nan na Fabarairu.

An shirya yin zanga-zanga a wajen majalisar dokokin kasar yau Litinin karkashin maudu’in #FreeSenegal a shafin X.

Tsohuwar Fraiminista kuma yar takara ta bangaren hamayya, Aminata Toure wadda aka kama a zanga-zangar ranar Lahadi, ta tabbatar cewa an sake ta a wani sako da ta wallafa a intanet.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here