Babu tabbacin Osimhen zai buga wasan Najeriya da Afirka Ta Kudu

0
135
Osimhen
Osimhen

Alamu na nuna ba lallai ba ne dan wasan Najeriya Victor Osimhen ya buga a Wasan Kusa da na Karshe tsakaninsu da Afirka ta Kudu a Gasar Kofin Afirka (AFCON 2024).

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ’yan Najeriya ken neman Super Eagles, musamman Osimhen da Lookman su huce musu haushinsu bayan mawakiyar Afirka ta Kudu Tyla ta doke mawakan Najeriya hudu wajen lashe kambin mawakan duniya na Grammy a ranar Lahadi.

Da misalin karfe 6 yamma ranar Laraba Super Eagles za ta barge gumi da Afirka ta Kudu a gasar da ke gudana a kasar Kwaddibuwa.

Idan Super Eagles Afirka ta yi rashin nasara a wasan, to Afirka ta Kudu ta yi wa Najeriya duka biyu ke nan a cikin kwana uku, a fannin waka da kuma kwallon kafa.

A ranar Litinin Super Eagles ta sanar cewa Osimhen na fama da rashin lafiya kuma sauran ’yan wasan sun tafi birnin Bouaké, inda za su fafata da Bafana-Bafana na Afirka ta Kudu.

Jami’in yada labaran tawagar ’yan wasan Najeriya, Babafemi Raji, ya ce “sauran ’yan wasan sun bar Osimhen a birnin Abidjan inda likitoci ke lura da shi; Amma idan ya samu sauki, to zai same su kafin karfe 5 na yamma.”

Masoya kwallon kafa a Najeriya dai na son ganin Gwarzon Dan Wasan Afirkan a wasan, ganin yadda ya nuna hazaka a sauran wasannin gasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here