Majalisar Senegal ta amince da tsawaita zaben kasar zuwa watan Disamba

0
117

Majalisar Senegal ta kada kuri’ar amincewa da dage lokacin gudanar da babban zaben kasar zuwa nan da watan Disamba, dai dai lokacin da ake ci gaba da ganin boren al’ummar kasar wadanda ke kone-kone kan tituna da nufin nuna adawarsu da matakin dage zaben.

Yayin zaman kada kuri’ar wanda ya kai har cikin dare a jiya Litinin ‘yan majalisu 105 ne suka goyi bayansa yayinda guda ya kalubalance shi, zaman da ya gudana bayan korar bangaren adawa daga zauren, batun da ya kara harzuka masu gangamin.

Fargaba ta baibaye yiwuwar dawowar zaman lafiya a Senegal sakamakon tsanantar boren tun bayan sanarwar shugaba Macky Sall a karshen mako da zuwa yanzu ya kai ga kame tarin masu zanga-zangar.

Matakin majalisar kasar ta yammacin Afrika ya bude hanya ga Sall ya ci gaba da jagoranci har zuwa karshen shekarar nan, duk kuwa da kiraye-kirayen manyan kasashe wajen ganin shugaban bai yi karan tsaye ga demokradiyya ba.

Bangaren adawa dai da suka bayyana matakin Sall da juyin mulki, Ayib Daffe ya ce kai tsaye matakin cin mutunci ne ga demokradiyyar Senegal dama kimar kasar baki daya.

Yanzu haka dai mahukuntan Senegal sun sake girke tarin jami’an tsaro a manyan tituna a kokarin dakile tarzomar, sai dai matasa na ci gaba da kone-kone tare da arangama da jami’an tsaro a kusan dukkanin biranen kasar.

RFI

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here