‘Nijar da Mali da Burkina Faso ba su cika ka’idar fita daga kungiyar mu ba’ – ECOWAS

0
217
Tinubu ECOWAS

Ƙungiyar Raya Tattalin Arzkin Ƙasahsne Afirka ta Yamma ECOWAS, ta ce dole ne ƙasashe Mali da Burkina Faso da kuma Jamhuriyar Nijar sun cika sharuɗan ƙungiyar kafin ta ba su damar ficewa daga cikinta.

Ƙungiyar ta ɗauki wanna mataki ne ranar Alhamis lokacin taron kwamitin sasanta wa na ƙungiyar da ka gudanar a Abuja babban birnin Najeriya.

Ranar 28 ga watan Janairu ne dai ƙasashen uku suka bayyana ficewarsu daga ƙungiyar, sannan suka aike mata da takardar ficewar tasu kwana guda bayan haka.

Yayin da yke jawabi a wajen taron shugaban hukumar gudanarwar ƙungiyar, OmarAlieu Touray ya ce matakin da ƙasashen uku suka ɗauka na ficewa daga ƙungiyar sun ɗauke sh ne cikin gaggawa don haka ƙungiyar ba za ta amince da shi ba.

Ƙarƙashin dokar ƙungiyar, duk ƙasar da ke son ficewa daga cikinta dole ne ta bayar da sanarwa shekara guda kafin ranar ficewar. Ya ƙara da cewa ƙasashen uku ba su yi la’akari da irin yadda matakin zai shafi al’ummominsu ba.

Duka ƙasashen uku dai na ƙarƙashin mulkin soji.

Haka kuma ana sa ran ƙungiyar za ta ɗauki matki kan halin da siyasar Senegal ke ciki, inda shugaban ƙasar Macky Sall ya ɗage zaɓen shugaban ƙasar da aka yi shirin gudanar da shi cikin wannan wata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here