An kama ‘yar ta’adda yayin karbar kudin fansa a Taraba

0
170
Taraba State

Dakarun rundunar sojin Najeriya sun kama wata mata da ake zargin mai garkuwa da mutane ce a yayin da take ƙoƙarin karɓar kuɗin fansar wani mutum da aka sace a Jihar Taraba.

Haka kuma sun damke wani dan bindiga da ya shahara wajen safarar makamai da alburusai, wanda ya yi ƙaurin suna wajen yi wa masu aikata laifuka a Jihar Taraba da sauran sassan kasar nan fataucin makamai.

An gano cewa matar da ta shiga hannu ta auri wani kasurgumin mai laifi wanda shi ne mataimakin kwamandan ’yan ta’adda, marigayi Hana Terwase da jami’an tsaro suka kashe a shekarun baya-bayan nan.

Kakakin rundunar sojin, Laftanar Oni Olubodunde ya ce sojojin da ke aiki da sahihan bayanan sirri kan ayyukan dillalan makamai sun kama wanda ake zargin Joshua Dutse Idah mai shekaru 45.

Ya kuma bayyana cewa sojojin sun bi sawun wanda ake zargin, lamarin da ya kai ga kama shi a garin Ibbi da ke Karamar Hukumar Ibbi a jihar yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Jihar Kaduna.

Laftanar Olubodunde ya bayyana cewa, a yayin da ake yi masa tambayoyi, Dutse ya amsa cewa zai je Jihar Katsina ne domin kawo bindigogi kirar AK-47 waɗanda tuni an biya shi kafin-alkalami na kuɗin makaman.

Kakakin rundunar ya bayyana cewa an kama matar ce wadda ake zargi da yin garkuwa da mutane mai suna Janet Igohia, mai shekaru 31 bayan ta karɓi kuɗin fansa na naira miliyan 1.5 na wani mutum da aka sace a yankin Chanchangi da ke Karamar Hukumar Takum ta jihar.

Igohia, ya bayyana cewa matar ta auri Voryor Gata, wani fitaccen mai laifi kuma tsohon shugaba na biyu ga marigayi Gana Terwase.

“A halin yanzu tana auren shugaban kungiyar masu tsatsauran ra’ayi a Kudancin Taraba.

“A cewarta, a baya ta auri wasu manyan masu aikata laifuka irin su marigayi Terkibi Gemaga wanda aka fi sani da Mopol, wanda ya yi kaurin suna wajen garkuwa da mutane da sojoji suka kashe shekaru biyar da suka gabata.

“Ta bayyana cewa ta kuma auri marigayi Gana Terwase, wani kasurgumin mai laifin da aka kashe a wani samame na hadin gwiwa shekaru uku da suka wuce,” inji shi.

Laftanar Olubodunde ya kuma bayyana cewa sojojin da aka tura a unguwar Mararaba Baissa a Karamar Hukumar Donga sun kama wasu mutane biyu da ake zargin ‘yan bindiga ne da ake zargi da aikata laifin kisan kai da kuma satar shanu da kuɗi N600,000.

Ya kara da cewa “Kuɗin da aka kwato daga hannun waɗanda ake zargin wani bangare ne na kuɗaɗen da suka samu daga haramtattun ayyukansu da kuma wayoyin hannu guda 2 kirar Techno.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here