Dalibai kusan miliyan 16 na kashe Naira Biliyan 159 duk wata a sayen data – Rahoto

0
117
Dalibai

Daliban Nijeriya da suke matakin karatu a karamar sakandari da wadanda suke karatun gaba da sakandari a manya-manyan makarantu daban-daban na kashe kimanin zunzurutun kudi da ya yawansa ya kai naira biliyan 159 wajen sayen datar waya a kowace wata, kamar yadda LEADERSHIP ta binciko.

A cewar bayanan da suke akwai, akwai adadin daliban sakandari miliyan 13.9 a makarantun gwamnati da na masu zaman kansu a fadin kasar nan, sannan, akwai wasu neman shaidar kammala digiri su miliyan biyu da suke manyan makarantu a fadin kasar nan.

Dalibai da dama da suka zanta da jaridar LEADERSHIP sun tabbatar da cewa a yanzu su na kashe a kalla naira dubu goma (N10,000) wajen sayen data a wata daya sakamakon tsadar data da kuma rage kima (Saurin zukewa da karewar data) da ake fama da shi a halin yanzu da ya mamaye dukkanin manyan layukan sadarwa guda hudu da suke baza hajarsu a Nijeriya.

Wadannan dalibai su miliyan 15.9 da suke kashe naira biliyan 159, na nuni da cewa, adadin naira dubu goma kowani dalibi yake kashewa a mallakar datar amfani da waya duk wata, kamar yadda binciken da LEADERSHIP din ta gudanar ya nuna.

Kazalika, da aka zurfafa bincike an gano cewa wasu makarantun sakandari sun rungumi tsarin koyo da koyarwa ta tangaru wato ta yanar gizo, su ma wasu jami’o’i da kwalejojin kimiyya da fasaha hadi da sauran manyan makarantu na amfani da tsarin koyarwa ta yanar gizo, lamarin da kai tsaye ya kara ninka amfani da data da dalibai ke yi har ma bayan karewar cutar nan ta Korona.

Wannan, kari ne kan manhajojin da daliban ke amfani da su a kafafen sadarwar zamani, musamman kafafen YouTube, TikTok, Facebook da twitter, hadi da saura gami da uwa-uba matambayi baya bara wato Google doin binciken ilimi.

Wasu, musamman daliban da suke gabar kammala karatu suna kashe kudade sosai wajen gudanar da bincike domin gudanar da aikin kammala makaranta wato projects.

Kan hakan, dalibai a Nijeriya na kashe naira tiriliyan 1.908 a cikin watanni sha biyu na shekara, wannan matakin, ya bai wa manyan kamfanonin sadarwa musamman MTN, Glo, Airtel da 9mobile damar samun maguden kudade ta hanyar amfani da data a kasar nan.

Bisa wannan, daliban da suke manyan makarantu a Nijeriya sun koka gaya kan yadda suke kashe makuden kudade duk wata, suna masu cewa, ba su ganin datar kudinsu, don haka ne suka zargi kamfanonin sayoyin salulu da bullo da hanyoyin da suke kalube musu kudade ala-tilas.

Bugu da kari, sun yi kira ga hukumar sadarwa ta Nijeriya (NCC) da ta kaddamar da bincike na musamman kan dalilan da suke janyo ninkuwan data da sauran bangarori a kamfanonin sadarwa.

Karuwar amfani da data da tsadarsa dai wanda masu amfani suka nuna cewa bai da tsawon da ke iya jima musu, ya zama babban abun damuwa da dalibai har da ma da ‘yan Nijeriya ke kokawa a kai, lamarin da ke tilasta wa mutane sayen data mai tsada domin samun damar shiga manhajoji ko kafafen da suke da bukata a cikin lamuran rayuwa na yau da gobe. Kazalika, masu amfani da layukan na iya bakin kokarinsu wajen sake sayen data kafin wanda suke da shi ya kare, domin kuwa da zarar ya kare ba za su samu damar shiga kafafen da suke da buri ba domin bincike ko wani abun na daban. Wannan batun, ya sanya ‘yan Nijeriya da dama daga muryoyinsu da yin korafi.

A misali, wani dalibi a jami’ar Legas (LASU), Prosper Adegun, ya ce, yana barnatar da kimanin naira dubu 8,000 zuwa 10,000 a kowace waya guda wajen mallakar datar amfani.

“Wannan ya ma zarce abun da na ke kashewa wajen ciyar da kaina, a kowace wata fa. Babu shakka, data na cikin rayuwarmu, amma a zahirin gaskiya ninkuwa da karin da ake samu na data abun damuwa ne matuka gaya. Zan yi farin ciki matuka idan har NCC za ta tashi tsaye ta yi wani abu kan wannan lamarin,” Adegun ya shaida.

Oladipupo Ramadan, dalibi ne da ke matakin aji biyu a jami’ar LASU, ya ce: “A ‘yan shekarun baya kalilan, ina iya amfani da 2GB kuma yana kaini har wata guda, amma a yanzu 6GB ma ba ya isa na. Idan har data wani abu ne, ni zan iya rayuwata ba tare da shi ba, idan har zai ci gaba da lakume min kudade. Abun bakin ciki da takaici, sannu a hankali datar ya zama abun amfanin dole a garemu.”

Wani dalibin aji 3 a jami’ar Obafemi Awolowo Unibersity (OAU), Ile-Ife da ke jihar Osun, Femi Adewoye, wanda ya dogara da data wajen yin bincikensa, halartar darasin aji, da kuma kasancewa tare da abokai da ‘yan uwansa, ya nuna bakin cikinsa kan yadda data ke lakushe masa kudade.

Ya ce: “Ina rasa data a karshen wata, kuma rashin datar na shafan karatuna da yin aikin aji. Kudin da nake kashewa wajen sayen data ya wuce misali. Akwai bukatar kamfanonin sadarwa su nemo hanyoyin magance wannan matsalar.”

Kan zargin wawushe data fiye da kima, hukumar kula da kamfanonin sadarwa, NCC, ta ce, korafin kwashe wa mutane data shi ne muhimmin korafin da hukumar ta samu daga wajen masu amfani da layukan waya a Nijeriya. Ta ce, mafi yawan korafin na zuwa ne kan yadda ake zuke wa mutane data sakamakon sauyi zuwa 4G da 5G/LTE.

Hukumar ta ce za ta yi abun da ya dace wajen shiga tsakani domin neman sauki kan yadda data bai tasiri ga mutane kasa.

Da ya ke karin haske, daraktan tabbatar da karfin network na NCC, Injiniya Edoyemi Ogoh, ya ce wasu nau’ikan fasaha na iya janyo warwareshe data ga masu amfani da layukan sadarwa.

Ogoh, wanda ke magana a wajen taron ganawa da masu amfani da layukan sadarwa karo na 91 da NCC ta shirya, ya ce, a halin da ake ciki na karin hanyoyin fasaha, mutane kan shiga website domin karanta wani abu ko bincike kai tsaye wasu abubuwa kamar bidiyo za su bude domin haka masu mallakin shafin suka sanya.

Ya kara da cewa sauran abubuwan da suke shanye data a buye sun hada da manhajoji da suke sabunta kansu da kansu da wayoyin zamani masu nadan hotuna da bidiyo.

Masanin ya kara da cewa sauran bangarorin da ke janyo rashin nagartar data sun kunshi sauyi da hanzarin karfin internet da aka samu sakamakon sauyi zuwa 4G, wanda kai tsaye ke sauke bidiyo da tsarin nauyinsa.

Kazalika, CEO kuma babban mataimakin shugaban NCC, Dakta Aminu Maida, ya shelanta cewar daga watan Janairun wannan shekarar za su bazama sanya ido kan ayyukan manyan kamfanonin sadarwa guda hudu da suke Nijeriya domin tabbatar da ayyukan da suke yi, sun yi daidai da ra’ayoyin al’umman kasa.

Maida ya kuma bada tabbacin cewa za su zauna da masu gudanar da kamfanonin sadarwa domin lalubo bakin zaren magance matsalolin.

“Zan zauna da shugabannin kamfanonin sadarwa, zan nusar da su su gane cewa a ko’ina mutum take, akwai bukatar yake ganin alfanu da tasirin kudin da yake zubawa cikin layukan sadarwa. Eh akwai matsaloli da dama kamar na nasu dizel da matsalolin tsaro, amma ba za mu tsame hannayenmu mu yi gum ba tare da yin komai ba.”

Kan masu amfani da layukan, Maida ya ce, za su bazama wayar da kan mutane kan hanyoyin kauce wa barnata datarsu ba tare da sun sani ba, “muna sayen manyan wayoyi da suke zuwa da manhajojin da suke sabunta kansu, akwai bukatar a zaunar da mutane a wayar musu da kai.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here