Shettima zai jagoranci wakilan gwamnati zuwa kallan wasan karshe na Super Eagles

0
122

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya umarci mataimakinsa Kashim Shettima ya jagoranci tawagar shugaban ƙasa zuwa wasan ƙashen na gasar Kofin ƙasashen Afirka (AFCON) da ke gudana a ƙasar Ivory Coast.

Cikin wata sanarwar da mataimaki na musamman ga shugaban ƙasar kan sadarwa, Stanley Nkwocha ya fitar, shugaba Tinubu ya buƙaci tawagar Super Eagles ta Najeriya, ta yi duk mai yiwuwa don sanya ‘yan ƙasar alfahari da tawagar a nahiyar Afirka.

Mataimakin shugaban ƙasar ya wakilci shugaba Tinubu a wasan kusa da na ƙarshe da ƙungiyar ta doke Afirka ta Kudu a tsakiyar mako.

Tawagar ta Najeriya dai za ta yi gumurzu da mai masaukin baƙi, Ivory Coast a wasan ƙarshe ranar Lahadi 11 ga watan Fabrairu.

Ƙasashen biyu dai sun fafata a wasan cikin rukuni a wannan gasar, inda Najeriya ta yi nasara da ci 1-0.

”Ƙwallon ƙafa ke taka rawa wajen haɗa kan ‘yan ƙasa, kuma rawar da tawagar super Eagles ta taka wajen ƙarfafa haɗin kai tsakanin ‘yan Najeriya ya tabbatar da haka”, in Tinubu.

Shugaban na Najeriya ya ce ya yi imanin zuwa wasan ƙarshen da mataimakinsa da sauran ‘yan tawagarsa za su yi, alama ce da ke tabbatar da goyon bayan gwamnatin ƙasar ga tawagar Super Eagles kan sadaukarwa da nasarorin da take yi.

Haka kuma gwamnatin ƙasar ta yi kira ga ‘yan Najeriya da ke ciki da wajen ƙasar da su haɗa kansu wajen nuna goyon baya ga tawagar ƙasar, ta hanyar furta kalaman ƙarfafa wa ‘yan wasan gwiwa, domin samun nasara a wasan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here