‘Yan ta’adda na barazanar hallaka ni – Dikko Radda

0
114
Umar Dikko Raɗɗa
Umar Dikko Raɗɗa

Gwamnan Katsina Malam Umar Dikko Radda ya bayyana cewar ‘yan ta’addan da jami’an tsaro suka hana sakewa a jihar na farautar sa, amma kuma hakan ba zai sa ya daga kafa a kokarin sa na kakkabe su daga jihar domin tabbatar da zaman lafiya ba.

Gwamnan yace rahotannin tsaron da yake samu na tabbatar da haka, amma ko da sunan wasa babu abinda zai razana shi wajen ganin ya kauda kai daga alkawarin da ya yiwa jama’ar jihar sa na samar musu zaman lafiya.

Rada ya bayyana cewar nasarar da ake samu a kan ‘yan ta’addan shi ne ke musu zafi, saboda haka jami’an tsaro za su ci gaba da aikin su wajen ganin an samu cikakken zaman lafiya a jihar.

Gwamnan ya kuma bayyana matukar damuwa a kan yadda ake safarar abinci daga Najeriya zuwa kasashen makota, abinda ke haifar da tsadar sa yanzu haka.

Yayin gudanar da wani taron gaggawa na jiga jigan ‘yayan jiharsa domin tattauna wasu daga cikin matsalolin da suka addabe ta, cikin su harda da matsalar tsaro da kuma tsadar kayan masarufi, Radda ya yi alkawarin kafa kwamitin da zai aiwatar da yarjejeniyar da taron manyan mutanen jihar ya cimma.

Yayin taron wanda ya samu halartar manyan sarakunan jihar, wato Dr Abdulmumini Jibrin, Sarkin Katsina da Dr Umar Faruk, Sarkin Daura da kuma shugabannin hukumomin tsaro, gwamnan yace duk da yake ba’a samu irin wannan zanga zangar a Katsina ba, yana da kyau a dauki mataki ganin yadda aka gudanar da ita a wasu jihohi cikin su harda jihar Kano dake makotaka da Katsina.

Jihar Katsina na daya daga cikin jihohin dake fama da matsalar tsaro a yankin arewa maso yammacin Najeriya, amma kafa rundunar ‘yan sakai ya fara haifar da ‘da mai ido wajen kakkabe ‘yan bindigar da suka hana zaman lafiya a wasu kananan hukumomin jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here