Jarumar shirin Dadin Kowa Bintu ta rasu 

0
138

Allah Ya yi wa jarumar Kannywood, Fatima Sa’ida wadda aka fi sani da Bintu ta shirin Dadin Kowa rasuwa.

Jarumar ta rasu ne bayan ta sha fama da rashin lafiya.

Wannan na cikin wani sako da Shugaban Hukumar Fina-Finai da Ɗab’i na Jihar Kano, Abba El-Mustapha ya wallafa a shafinsa na Instagram.

Tuni aka yi jana’izarta kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar, a unguwar Gunduwawa da ke Kano.

Bayani na tafe

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here