Tsadar rayuwa: Zanga-zanga ta barke a Legas 

0
95

Dandazon mutane sun tare hanyoyi tare da yin zanga-zanga a Jihar Legas, don nuna damuwarsu kan yadda rayuwa ta yi tsada a kasar nan.

Mata da matasa ne suka yi zanga-zangar a yankin Ibeju-Lekki da ke jihar a ranar Asabar.

Mutanen na dauke da alluna da rubutu daban-daban, inda suke kiran Shugaba Tinubu da ya kawo musu dauki.

“Baba Tinubu, ‘yan Najeriya na cikin yunwa, Tinubu ka kawo mana dauki.”

Wannan zanga-zangar na zuwa ne bayan wadda aka gudanar a jihohin Kogi, Osun, Neja da kuma Jihar Kano kan tsadar rayuwa a kasar nan.

Tun bayan cire tallafin man fetur a watan Mayun 2023, farashin kayan masarufi suka yi tashin gwauron zabi a Najeriya.

Hakan ya sanya masu karamin karfi shiga tsaka mai wuya, inda suka damuwa kan yadda farashin kayayyaki ke kara kudi.

Sai dai a gefe guda kuwa, Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewar tana duk mai yiwuwa don ganin an samo daidaituwar farashin kayayyaki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here