‘Yan sanda sun kashe wasu gawurtattun ‘yan ta’adda a Abuja

0
58

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami’anta sun yi nasarar kashe gawurtattun masu garkuwa da mutane da dama da suka addabi wasu yankunan Abuja babban birnin ƙasar.

Kakakin rundunar ACP Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar da yamma.

Rundunar ƴan sandan ta ce cikin ƴan bindigar da ta kashe har da Musa Wada (Sabo) Magaji, wani gawurtaccen mai garkuwa da jama’a.

“Da sanyin safiyar 9 ga watan Fabrairun 2024, jami’an leƙen asiri na rundunar ƴan sandan Najeriya (FIB-IRT), bisa samun bayanan sirri, sun yi nasarar kai hari tare da kashe gawurtattun masu garkuwa da mutane da dama ciki har da fitaccen mai garkuwa da mutane Musa Wada (Sabo) Magaji, a yankin Mpape da ke Abuja,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta ce ƴan sandan sun kwashe kusan minti 30 suna gumurzu da ƴan bindigar lamarin da ya sa masu garkuwar da mutane da dama suka ji munanan raunuka, ko da yake ɗan sanda guda ɗaya ma ya jikkata.

Rundunar ƴan sandan ta ƙara da cewa ta samu nasarar ce bayan ta kawar da wani mai garkuwa da mutane mai suna Abubakar Wada, amini ga Musa Wada, wanda shi ne ya nuna wa jami’an ƴan sanda maɓoyarsa.

“Musa Wada, wanda aka fi sani da suna Sabo, shi ne ya kitsa satar mutane domin karɓar kuɗin fansa a wuraren da suka haɗa da Mpape da Bwari a Abuja; da Kagarko a Kaduna; da Masaka, da kuma ƙauyen Nukun da ke jihar Nasarawa”, a cewar sanarwar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here