NIS ta kara kaimin sintiri a Arewa Maso Gabas domin dakile karancin kayan abinci

0
97

Mataimakin Kwanturola Janar mai kula da shiyya ta uku (Zone C) da ta hade yankin arewa maso gabas mai shalkwata a Bauchi, ACG James Sunday, ya bayar da umarnin kara kaimin sintirin tsaron iyakokin kasa domin dakile silalewa da kayan abinci.

Umarnin a karkashin shiri na musamman mai taken “Operation Tsaron Iyaka” zai tabbatar da cewa kayan abincin da aka fi amfani da shi a gida kamar shinkafa, wake, albasa, doya da sauransu, ba a bi ta barauniyar hanya da su zuwa wasu kasashen ba.

ACG James Sunday ya ce daukar matakin ya zama wajibi saboda yadda ‘yan kasa ke fuskantar karancin abinci wanda ya zama wajibi NIS ta bayar da gudunmawa domin shawo kan matsalar.

A wata sanarwar manema labarai da ya aike wa LEADERSHIP Hausa, ACG James ya ce hukumarsu bisa hadin gwiwa da Hukumar Hana Fasa Kwauri ta Kasa za ta kara sa ido wajen tabbatar da cewa ba a fice da kayan abinci a tireloli da sauran manyan motoci ba illa wanda magidanta suka saya kawai domin ciyar da iyalansu.

Ya ce jami’ansu a karkashin Kwanturola Janar ta NIS, Caroline Wuraola Adepoju sun mike haikan wajen tabbatar da samun nasarar sintirin musamman yadda shugabarsu take kara musu kwarin gwiwa a kan su jajirce wajen nuna kishin kasa a bakin aiki.

Kwanturololin NIS da ke yankin arewa maso gabas za su yi aiki kafada da kafada da takwarorinsu na Bauchi, Gombe da Filato domin musanyar bayanan sirri a kan duk wasu kayayyakin abinci masu yawa da ake safara a yankunansu inda hakan zai taimaka gaya wajen hana masu silalewa da abinci daga kasar nan cin karensu babu babbaka.

“Wannan wani mataki ne mai muhimmanci da ya zama wajibi mu dauka a NIS da ke shiyya ta uku (Zone C) tare da manyan ofisoshin da ke karkashin shiyyar domin mu taimaka wa gwamnati wajen yaki da safarar abinci ba bisa ka’ida ba wadda yake janyo karancinsa da karin wahalhalu ga ‘yan kasa.

“Jami’anmu tare da hadin gwiwar sauran hukumomi za su yi kokarin bankado masu kunnen kashi da ke haddasa karancin abincin ta hanyar safararsa ba bisa ka’ida ba, mun kimtsa tsaf domin tabbatar da tsaron iyakokin kasa a yankunan da ke karkashin kulawar NIS a shiyya ta uku (Zone C),” in ji ACG James Sunday.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here