Yau wa’adin biyan kudin hajjin bana a Najeriya ke cika

0
125

Yayin da yau ke zama ranar karshe da hukumar aikin hajji ta Najeriya ta bayar domin maniyyata su kammala biyan kudin kujerar hajji, bayanai sun nuna cewa da wuya ne kasar ta cike gurbin kujeru dubu cassa’in da biyar da hukumomin Saudiyya suka yi mata tanadi.

Rahotanni na cewa akwai maniyyata da dama da suka gaza biyan ko dai kafin alkalami ko ma biyan cikon kudin hajjin da NAHCON ta sanar.

Karyewar darajar takardar naira ta sa kudin kujerar aikin hajji tashi zuwa naira miliyan hudu da dubu dari tara daga kafin alkalamin naira miliyan hudu da rabi da hukumar aikin hajji ta Najeriya ta sanar.

A ranar 30 ga watan Janairu ne darajar naira ta yi faduwar da ba ta taba yi ba inda a hukumance aka sayar da ita a naira dubu daya da dari hudu da goma sha uku kan kowace dala guda.

NAHCON ta ce maniyyata hajjin bana daga kudancin Najeriya za su biya naira miliyan hudu da dubu dari takwas da dubu cassa’in da tara a matsayin kudin kujerar hajji yayin da wadanda suka fito daga arewacin kasar za su biya naira miliyan hudu da dubu dari shida da dubu cassa’in da tara sai kuma maniyyata daga Yola da Maiduguri da za su biya naira miliyan hudu da dubu dari shida da dubu saba’in da tara.

NAHCON ta ware kujeru dubu saba’in da biyar ga jihohi talatin da shida har da Abuja, babban birnin tarayyar kasar sai kuma kujeru dubu ashirin ga jiragen yawo.

Duk da cewa hukumar ba ta bayyana adadin maniyyatan da suka yi rajista a bana ba, wani bincike da jaridar DailyTrust ta gudanar ya nuna cewa galibin jihohin Najeriya ba su cike rabin kujerun da aka ware musu ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here