‘Yan kasuwar Kano sun musanta zarge-zargen boye kayan abinci

0
95
Kasuwar Kano

‘Yan kasuwan Kasuwar Singa a Jihar Kano sun yi kakkausar suka a kan zargin boye kayan abinci a rumbunansu domin su yi tsada sannan su fito da su kasuwa.

‘Yan Kasuwar sun musanta wannan zargin ne a wani taro da suka yi da shugaban hukumar karbar korafe-korafe da cin hanci da rashawa na jihar Kano (PCACC).

Da yake yi wa manema labarai jawabi bayan kammala taron, wani dan Kasuwar, Ibrahim Danyaro ya bayyana cewa, “Duk wani kasuwancinmu a bude mukeyinsa, ba wani boye-boye ko kuma yunkurin muzgunawa al’umma, ko kuma kuntatawa musamman wajen farashi.”

Rahotannin baya-bayan nan sun nuna cewa, hukumar PCACC ta kai samame a wasu rumbunan abinci guda biyar a kasuwar Dawanau, lamarin da ya haifar da fargabar tsakanin ‘yan kasuwar kano.

Shugaban hukumar, Barr. Muhyi Magaji Rimin-gado ya bayyanawa manema labarai cewa, ba wai suna wannan sumamen ba ne da nufin musgunawa ‘yan kasuwa, a’a, suna yi ne dan tallafawa al’umma da kuma saukaka musu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here