Rundunar yan sandan Najeriya reshen jihar Kano ta ce ta kama wani riƙaƙƙen “dillalin ƙwaya” da ta daɗe tana nema ruwa a jallo tare da wasu mutum takwas.
Wata sanarwa da kakakin rundunar SP Abdullahi Kiyawa ya fitar a yau Litinin ta ce sun yi nasarar kama Sadam Mu’azu, wanda aka fi sani da Badoo, ne bayan ƙorafe-ƙorafen da mazauna unguwar Takuntawa suka kai mata.
“An yi nasarar kama shi ne sakamakon bayanan sirri da kuma haɗin gwiwa da mazauna yankin wanda rundunar Anti-Daba ta jagoranta,,” in ji sanarwar.
Ta ƙara da cewa dakaru sun kama ƙarin mutum takwas daga cikin ‘yan tawagar matashin mai shekara 33, “waɗanda ke samun tabar wiwi daga kudancin ƙasar nan kuma yake rarraba wa mutane har da matan aure a gidaje”.
Haka nan, rundunar ta ce ta ƙwace ƙunshi 11 na abin da take zargin tabar wiwi ce, da gatari, da babura biyar da ake “amfani da su wajen rarraba kayan”, da kuma kuɗi naira 111,500 da ga hannunsu.
Za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike, a cewar rundunar.