Tubabbun ’yan ta’adda sun kai hari ofishin ’yan sanda a Maiduguri

0
132

Wasu tubabbun ’yan Boko Haram sun kai hari ofishin ’yan sanda a Maiduguri a kokarinsu na ƙwato ’yan uwansu da aka kama bisa kan laifin safara da shan miyagun kwayoyi.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar Borno, Kenneth Daso, ya ce jami’an da ke bakin aiki sun yi nasarar fatattakar maharan da suka zo da niyyar ko a mutu ko a yi rai.

Ya ce, “A ranar 30/04/24 da yamma, rundunar hadin gwiwa da ke sintiri a Kasuwar Fara, ta samu rahoto kan wasu masu safarar miyagun kwayoyi, da masu sha, da aka bincika sai aka samu tubabbun ’yan Boko Haram ne suke aikata waɗannan munanan ayyuka.

“An kama mutum takwas, maza bakwai da mace guda ɗaya, kuma an same su da gram 476 na miyagun ƙwayoyi.”

Sai dai ganau sun shaida wa wakilinmu cewa, maharan sanye da kayan sojoji suna dauke da  adduna da wuƙaƙe, suka kutsa ofishin ’yan sandan da karfin tsiya inda suka fitar da wasu tsararru.

“Kusan mahara 20 ne suka kutsa kai cikin ofishin ’yan sandan, inda suka tsere da wasu daga cikin waɗanda ke kulle,” in ji wani shaida.

Shi ma wani ganau ya bayyana cewa ’yan sandan da ke ofishin sun yi iyakacin kokarinsu wurin dakile harin amma abin ya fi i karfinsu.

“Wasu daga cikin ’yan sandan sun tsere, amma sun dawo bayan ƙarin wasu jami’an sun zo.

“Muna ganin cewa maharan ba su iya kubutar da wadanda ake zargin tubabbun ’yan ƙungiyar Boko Haram ɗin ba, sai dai wasu mutane daban da ke tsare a bayan kanta ne suka tsere”

Mazauna yankin sun ce sun tsorata da faruwar lamarin, inda suka ce lamarin ya nuna karara cewa babu tsaro a Maiduguri.

Fanta Modu, wanda ke da gidan abinci a yankin, ya bukaci gwamnati ta sake duba  tsarin Gwamnatin Tarayya na sauya tunanin masu tsattsauran ra’ayi.

A nata ɓangaren, gwamnatin jihar Borno ta ce kawo yanzu ba ta samu rahoton abin da ya faru ba.

A daren ranar Alhamis, Abdulrahman Bundi, daya daga cikin masu magana da yawun Gwamna Babagana Zulum, ya ce  ba a yi musu bayani kan lamarin ba don haka ba zai iya cewa komai ba.

“Na karanta labarin a shafukan sada zumunta. Ba ni da isassun bayanai amma ina mai tabbatar muku da cewa gwamnati za ta yi tsokaci kan lamarin bayan mun samu sahihin bayani kan abin da ya faru.”

Wani mai sharhi kan harkokin tsaro, Sanata Iroegbu, ya ce abin da ya faru, ya nuna buƙatar a sake duba batun dawo da tubabbun mayakan na Boko Haram cikin al’umma.

“Barazanar da ke tattare da wannan abin yanzu shi ne, abin da tubabbun ’yan Boko Haram suka yi ya gaskata fargabar masu adawa da nuna fargaba a kan shirin karɓar tuban ’yan Boko Haram tun da farko.

Kawo yanzu dai akwai dubban tubabbun ’yan ƙungiyar Boko Haram a sassan Jihar Borno da ma Najeriya baki ɗaya.

Sai dai faruwar wannan lamari ya sa mutane sun ƙara faɗawa cikin sabon fargaba kan mene ne zai biyo baya.

AMINIYA

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here