Kungiyoyin APC zasu kai Ganduje kara gaban kotu

0
96

Gamayyar kungiyoyin APC  dake Arewa ta tsakiyar sun bawa shugaban jami’iyyar na kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje wa’adin kwanaki 7 ya yi murabus daga mukamin sa.

Shugaban kungiyar Hon Saleh Abdullahi Zazzaga, ne ya sanar da daukar Wannan mataki a taron manema labarai da suka gudanar a Jos babban birnin jihar Plateau.

Ƙungiyar tace idan har wa’adin ya kare Ganduje bai sauka ba, to zasu iya daukar matakin shari’a a kansa.

Karanta karin wasu labaran:APC ta sake shigar da kara kan zaben kananun hukumomin Kano

Wa’adi zai kare a ranar Litinin 14 ga watan Oktoba, 2024.

Saleh Zazzaga, yace dalilin su na bayar da wa’adin shine a Wannan lokaci shugabancin jam’iyyar APC zai kasance an samar da shi daga arewa ta tsakiya kamar yadda aka tsara a lokacin babban taron jami’iyyar da ya gudana a ranar 26 ga watan Maris, 2022.

Ya kafa hujja da cewa Ganduje, ya fito ne daga arewa maso yamma, don haka dole ayi gyara ko su dauki matakan gyarawa da kansu, saboda an karya dokokin kundin tsarin mulki na APC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here