Hisbah ta kama matar da ke tara yan mata don lalata musu tarbiyya

0
68

Jami’an rundunar Hisbah ta jihar Kano sun kama wata mata mamallakiyar wani waje da ake tara yan mata suna yin rawa, shaye shaye da rashin tarbiyya a yankin Tashar Rami, dake unguwa uku a karamar hukumar Nassarawa.

Rundunar Hisbah tace al’ummar dake rayuwa a kusa da Wannan waje ne suka kai mata korafin irin abubuwan lalatar da ake aikatawa.

Sannan Hisbah tace matar tana dauko mata masu zaman kansu zuwa Kano daga jihohi daban daban, don yin shaye shaye, da karuwanci.

Karanta karin wasu labaran:Hisbah ta musluntar da macen da tazo Kano yawon banza

Mukaddashin babban kwamandan rundunar Dr Mujahiddin Aminudden, yace matar dake tara yan matan ba yar Jihar Kano ce ba, tazo ne don tara yan mata ayi fasikanci dasu ita Kuma tana samun kudi, inda yace bayan kama ta zata fuskanci hukunci.

Haka zalika a unguwar Na’ibawa Hisbah ta kama masu wasu gidaje guda biyu da ake biyan su ana kai yan mata ana lalata tarbiyyar su.

Hisbah taja hankalin al’umma su zama masu kiyaye dokokin Allah saboda rashin bin ka’idar muslinci ne yake kawo fitina a cikin al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here